A Yau Assabar 1-12-2018 Ne Akayi Bikin Bayyana Sakamakon Buhun Gero Da Wasu Matasa Su 37 Suka kwashe Watanni Wato Kwana 107 Suna kirga A Yauri Ta Jihar KEBBI Bayan Gardama Data Kaure a Tsakaninsu Inda Wasu Sukace Mutanen Nigeria Sunfi Yawa Wasu kuma Sukace A'a Buhun Gero Yafi Yawa.
Hakan Yasa A kafara kirga Hatsin A kwaya Daya Bayan Daya Ta Buhun Inda A Yau Akayi Bikin Bayyana Sakamakon A Fadar Mai Martaba Sarkin Yauri. DR. ABDULLAHI ZAYYANU Inda Sarkin Yana Daga Cikin Wadanda Suka halarci Wurin Tareda Shehun malami Na Jami'ar Usmanu Dan Fodio Wato PROF. ALIYU MUHAMMAD BUNZA Na Fannin Harshen Hausa Da Kuma Commissioner Na Watsa Labarai Na Jihar Kebbi Daya Wakilci Gwamna.
Sakamakon BUHUN GERO An Samu.
Miliyan goma sha daya, da Dari tara da saba'in da tara, da dari takwas da sittin da takwas(11,979,868) ke kicin Buhun Gero.
(11,979 868) Eleven million, nine hundred and seventy nine thousand, eight hundred and sixty eight 11,979,868
COPIED FROM ✍ MUDASSER SANI BIRNIN KEBBI
