-->

Saturday, 3 August 2019

YADDA AKE AMFANI DA SUPER STATUS SAVER

Super Status Saver wani sabon android application ne wanda zaka iya yin abubuwa da dama da shi ba iya status saving ba. Abubuwan da zaka iya yi da shi sun hada da:

1- Canza fonts
2- Text Repetition
3- Tura Empty message
4- Tura message ba tare da kayi saving number ba
5- Status saving


1- Yin rubutu cikin salo ta hanyar amfani da emojis na wayarka. Yadda zaka yi shine zaka bude app din, bayan ka bude shi zai bude maka menu kamar haka

Sai kayi clicking akan TEXT TO EMOJI zai bude maka sabon shafi, sai ka rubuta text din ka. Misali: "Hi" sai ka sauko kasa ka zabi kalan emoji da kake son app din yayi amfani da shi sai kawai kayi clicking convert... Idan an duba a wannan hoton ni heart emoji na zaba don haka rubutun ya fito kamar haka:


Bayan yayi converting sai kayi clicking akan share zai nuna maka duk whatsapp contact naka, sai ka zabi wadanda kake son tura mawa. Ko kuma kayi copying a clipboard dinka Sai ka shiga whatsapp ko Facebook ko telegram ko ma dai duk inda kake bukata sai kaje kayi pasting, shikenan.

2- Abu na biyu da zaka iya yi shine TEXT REPETITION. Maimaita wani rubutu da kayi zuwa adadin yawan da kake bukata. Misali kana son maimaita ma budurwar ka kalmar 'I love you' kamar sau dari biyu a cikin message daya. Anan maimakon kayi ta maimaitawa kawai zaka shiga TEXT REPEAT ne, sai ka rubuta 'I love you... Sai kayi switching new line ma'ana kana son kowane I love you ya kasance akan sabon layi ba a cakude ba, sai ka sauko kasa ka rubuta adadin yawan da kake son ya maimaita maka, sai kayi clicking akan repeat anan take zai maimaita maka text dinka sau adadin da kake bukata kamar yadda kake gani a wannan hoton



3- Abu na uku shine sanin kowa ne a whatsapp ba'a iya tura empty message dole sai ka rubuta koda full stop symbol ne.. To ta hanyar amfani da super Status Saver zaka iya wannan. Sai dai kawai abokin ka yayi receiving alert cewa ka turo message sai ya bude sai yaga empty.

Yadda ake yi shine zaka yi clicking akan BLANK MESSAGE sai ka zabi adadin empty layi nawa kake bukata ko biyar, ko goma, ko ashirin duk dai yadda kake bukata sai kawai kayi copying kaje kayi pasting ma wanda kake son tura mawa ko kuma kayi sharing daga app din.


4- Abu na huɗu da zaka iya yi shine zaka iya aika DIRECT MESSAGE. Ma'ana zaka iya tura message zuwa kowace number ba tare da kayi saving na number din a wayar ka ba.
Zaka yi clicking akan direct message zaka ga page ya bude maka da wani column an rubuta 91 sai ka cire 91 din kayi replacing da 080 ko 070 ko dai lambobin da suka fara da lambar da zaka tura ma message.. Sai ka karasa rubuta cikon lambobin wayar da zaka tura ma sakon shike nan sai ka sanya send....



Anan zai kaika cikin inda zaka rubuta sakon da kake son turawa.


5- Abu na biyar shine status saving wanda zaka iya saving duk status din da friends din ka suka ɗora. Yadda zaka yi shine zaka bude whatsapp din ka, sai ka kalli duk hotuna da videos din da kake son saving.

Daga nan sai ka fita daga whatsapp ka shiga super Status Saver din ka, automatically zaka ga duk hotunan daka kalla a whatsapp din ka. Idan videos kake bukatar saving sai kayi clicking akan videos daga gefen hagu sai kayi clicking akan download icon a gefen hagun screen din ka. Idan kana son viewing next video Sai kayi clicking akan next.

 Ku shiga nan ku sauke Super Status Saver
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.saifmanstudio.SuperStatusSaver
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner