-->

Saturday, 24 November 2018

YABON DA KAFIRAI SUKA YI MA ANNABI MUHAMMAD S.A.W

Assalamu alaikum yan uwa barka da hidima da kokari wajen bikin maulidin Muhammadur Rasulullahi.

Yan uwa ko kun san abinda babban marubuci Michael Hart ya fada game da annabin mu? To a takaice dai Michael Hart wani shahararren marubuci ne wanda wanda ya shafe shekara 28 yana rubuta wani babban littafi wanda ya sanya ma suna THE 100 MOST INFLUENTIAL PEOPLE ma'ana mutane ɗari da suka fi kowa fada a ji a duniya. Bayan ya kammala tattara su, sai ya sanya Annabi Muhammadu na farko wato duk ya zarce sauran kenan.


Ashe abin yayi ma kafirai yan uwansa da majiya annabi zafi, don haka wata rana Michael Hart yana gabatar da lacca a babban birnin Birtaniya wato London, sai ake tambayar shi wai saboda me ya sanya annabin musulmai a cikin masu fada a ji na duniya kuma wai ya sanya shi farko ma.

Sai yace "Annabi Muhammad yayi da'awar annabta a shekara ta 611 miladiyya wanda a lokacin mutum hudu ne kacal suka yi imani da shi, daga babban abokinsa sai matarsa sai yara guda biyu. Wannan ya faru sama da shekara 1400 da suka gabata amma a yau yawan musulmi ya haura mutum biliyan daya kuma har yanzu hauhawa suke yi ba raguwa ba.

Da wannan na gane tabbas ba makaryaci bane don karya ba zata taba ƙarkon shekara 1400 ba, kuma babu yadda za'a yi har mutum sama da biliyan daya duk su ruɗu akan karya.

Hakanan kuma duk da wannan tsawon lokacin da aka dauka miliyoyin musulmai a shirye suke su sadaukar da rayukansu saboda kalma daya tak ta batanci ga annabinsu".

Sai ya dakata yace "a yanzu ko akwai wani kirista daya tak da yake iya bayar da rayuwarsa idan hakan ta faru ga Yesu Almasihu?" 

Anan sai kowa yayi tsuru-tsuru... 

Don haka mu musulmi wallahi mu gode ma Allah da ya bamu annabi Muhammadu, kuma mu sani wallahi ba mune muka yi ma annabi gata ba, shine yayi mana gata.... 

Allah ka kara mana soyayyar ma'aiki S.A.W

Babu laifi don ka kwafa ka yaɗa, ko kace daga shafin mu ka kwafo ko karka fada duk daya, mu dai saboda Rasulullahi muka yi. 
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner