Bloggers da yawa musamman ƙanana irin mu, muna fama da ƙarancin page views. To zaka iya kara yawan page views ta hanyar amfani da auto refresh feature zaka iya boosting traffic din ka da kusan kashi 40 cikin 100.
Yadda zaka sanya auto refresh feature a blog din ka shine:
1- Ka shiga blogger dashboard naka
2- Ka shiga theme
3- Ka shiga edit html
4- Sai kayi pasting wannan code din a karkashin
<head> na blogger template naka.
<meta content='300' http-equiv='refresh'/>
Sai kawai kayi saving.
KARIN BAYANI
Wannan 300 din da kake gani a cikin code din tana nufin kana bama duk browser din data ziyarci shafin ka da ta riƙa refreshing duk bayan second 300 wanda yake daidai da mintuna biyar kenan.
To anan yadda abin yake duk refresh daya da browser zata yi za'a kidaya shi a matsayin page view daya. Haka kuma zaka iya kara tsawon seconds din da kake bukata ko kuma ka rage.
Wannan ga wanda yake da adsense a site nasa tamkar auto impression ne saboda duk wanda ya ziyarci Blog naka koda ba wani abu yake ba to browser dinsa zata yi ta tara maka page views tare da impression.
