-->

Wednesday, 15 November 2017

YADDA ZAKA BUDE ACCOUNT DIN BANKI NA GTBANK DA WAYAR KA.

Duba da matukar amfanin account din banki, a yau naga ya dace mu yi ma mutane dan takaitaccen bayanin yadda zasu iya bude Account din banki da kan su alhali suna gida a kwanciyar su ba tare da wani wahala ba. A yau kusan ko me kake son yi idan baka da bank account sai kaga abin yana nema yafi karfin ka. Ya ishe ka misali har yanzu maganar da nake maka akwai wadanda ke karkashin tsarin Npower kusan cikin shekara ta biyu suke amma har yanzu basu fara karbar ko sisin kwabo ba, kasancewar rashin takamaimai din account din banki. Mafiya yawan wadanda suka gamu da wannan matsalar kodai ya kasance sun yi amfani da Account number din wani, ko kuma account din da suka sanya ya lalace wato ya zama dormant.

A wannan zamanin ina mamakin ganin matashi cikakke wanda ya kai kimanin shekara ashirin abinda yayi sama wai baya da bank account. Mu sani bank account ba lallai sai ma'aikata ko masu wani yawan transactions na kudi bane kawai ke iya bude Account kowa zai iya budewa saboda tsaro dani gudun ko ta kwana.

Ba tare da bata lokaci ba zan tafi kai tsaye kan yadda zaka bude Account din cikin sauki ta hanyar amfani da wayar ka ta hannu ko ma wace iri ce kai in takaice maka koda kuwa Nokia torchlight ce.


Ga wanda yake bukatar bude Account na GTBANK sai kawai ya latsa *737# ya sanya kira. Bayan tayi loading zasu bashi menu kamar haka

1. Airtime-self
2. Airtime-others
3. Buy data
4. Transfer funds GTBANK
5. Transfer funds other banks
6. Account Balance
7. Create/change pin
8. Next

To anan ba tare da bata lokaci ba sai a latsa 8 sannan ka sanya OK na wayar ka. Zai bude maka wani fejin mai kama da na sama kamar haka:

1. Cardless withdrawal
2. Open account
3. Cheque status
4. Salary advance
5. Loan balance
6. Generate token
7. Deposit and withdrawal

Anan sai kayi reply da 2 sai ka sanya Okey. Zasu sake baka options kamar haka:

1. Used BVN details
2. Supply details

Idan kana da BVN already sai kawai ka danna 1 tare da OK. Nan take zasu yi searching din BVN details naka kamar suna, shekarar haihuwa, lambar waya, address, hoto tare da finger print. Ba tare da wani bata lokaci ba zasu aiko maka da Account number din ka cikin abinda bai wuce minti biyu ba. Daga sun turo maka account number Shikenan ka kammala bude Account dinka sai kawai ka fara enjoying duk services din da bankin yake rendering ga abokan huddar su.

GA WANDA BAYA DA BVN KUMA

Idan suka baka wannan option din:

1. Used BVN details
2. Supply details

Sai ka danna 2 ka sanya OK zasu kai ka feji na gaba mai dauke da option kamar haka:

"ENTER FIRST NAME"
Sai ka rubuta sunan ka sai ka danna OK zai kai ka wani feji kamar haka:
"ENTER LAST NAME "
Sai ka rubuta sunan mahaifin ka, sai ka danna OK. Zasu bude maka wani feji haka:

"Do you have a middle name"
1. Yes
2. No

Wato kana da wani sunan bayan wadannan, ma'ana idan da suna uku kake bearing sai ka danna 1 sai danna OK zasu umarci ka sanya dayan sunan sai ka latsa OK. Idan kuma da suna biyu kake bearing sai kawai ka danna 2 ka danna OK. Daga nan zasu kai ka wani fejin kamar haka.

"Please select your gender"
1. Male
2. Female

Anan jinsin ka ake bukata kayi specifying sai maza su sanya 1 su danna OK, su kuma mata su danna 2 su sanya OK. Daga nan zasu tambaye ka DOB din ka ma'ana date of birth din ka Sai ka cike appropriately.

Kana gama cike wadannan details din zasu aiko maka da account number dinka. A wannan lokacin ma zaka iya antaya ma account din kudi don ajiya, sai dai ba zaka cirewa ba har sai kaje banki kayi enrollment na BVN tare da passport photograph da kuma national ID card, ko Tax identification ID, ko voters card.

Shikenan...
Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner