Bulk SMS wata hanya ce dake baka damar tura sakon SMS sama da dubu goma a lokaci daya tare da baka damar zaben sunan da kake son ya bayyana cikin wayar wanda ka tura mawa maimakon number dinka...
Bulk SMS a yau baya da bukatar wata gabatarwa kasancewar ya zama ruwan dare a cikin mu. Bulk SMS ne Bankuna ke amfani dashi wajen yi ma abokan huddar su alert. Bulk SMS ne kamfanoni da manyan ma'aikatun gwamnati ke tura ma ma'aikatan su don gayyatar interviews ko meetings dss. Da bulk SMS ake amfani wajen tura invitation na aure, engagement, haihuwa, rasuwa, ko kuma ma duk wani abu mai mahimmanci da ake son sanar da jama'a.
Muje aiki, idan kana son tura sakon bulk SMS akwai portals da yawa da suke sayarwa amma ni wadanda nafi amincewa dasu su ne www.smartsmssolutions.com da farko zaka shiga shafin nasu ta hanyar adireshin su dake sama sai kayi register. A wajen register din ana bukatar lambar wayar ka da kuma adireshin ka na email sai username da password.
Da zaran ka cike duk wadannan columns sai kawai ka sanya sign up ko register,. Nan take zasu baka kyautar SMS goma don ka jaraba.
YADDA ZAKA FARA AIKA SAKON
Shiga adireshin su ka sanya username da password, zai yi loading sa'annan ya bude. Da zaran ya bude zai nuna maka yawan SMS din ka da suka rage. Sai kayi clicking akan "Send SMS" zai bude maka wani Page din mai columns uku.
Column na 1- zaka sanya duk Phone numbers din da kake son tura ma sakon. Ka rika sanya comma tsakanin number da number. Kuma zaka iya tura ma number daya idan kana bukata.
Column na 2- Zaka sanya ainihin sunan da kake son ya bayyana a wayar wanda ka turawa maimakon number din wayar ka. (kar ya wuce alphabet 11)
Column na 3- Zaka rubuta sakon da kake son sanarwa
Danna send kawai shi kenan wanda ka turawa zai yi receiving in less than a minute.
YADDA ZAKA SAYI SMS UNITS
Suna sayar da duk SMS unit akan kudi 1.80 wato bai kai naira biyu ba ma kenan. Sannan suna daukar unit daya a duk SMS mai page daya wato 160 pages.
Idan kana son saye ka shiga "Buy SMS" zasu baka duk bank details din su wanda zaka tura musu kudi ko ta bank transfer ko ta direct deposit. Da zaran ka tura musu da zaran sun maka text cewa sun ga kudin ka don haka ga SMS dinka.
Kar ka manta idan zaka masu bank direct deposit to jikin teller dinka ka rubuta masu username dinka a matsayin depositor name.
Haka kuma zaka iya sayen SMS ta Quickteller
matukar kana da ATM card.
Feel free to ask questions

