A da duk wanda kaga yana hada apps ko na Android ko iOS ko Windows
to ka tabbata mutumin nan ya kai kwaro a fagen sanin ilimin programming, sai
dai a yanzu labarI yasha bamban don kuwa kowa zai iya hada application ba tare
da yasan komai a harkar programming ba. Ana yin hakan ne ta hanyar amfani da
wasu sanannun website da suke baka dama ka kirkiri application. Ire-iren
wadannan website suna nan birjik sai dai zamu takaita da kawo kwara biyar ne
kacal wadanda suka fi shahara da kuma saukin amfani.
1-
ANDROMO: andromo yana cikin manya kuma shahararrun
portals da ake amfani da su wajen creating applications irin na wakoki, ebooks,
website, rubutun zube da sauransu. Kusan ince kowa zai iya developing
application a Andromo. Da farko zaka yi register da su, daga nan zasu baka dama
kayi creating application daya don kaga yadda suke da saukin sha’ani. Bayan
kayi creating wannan app din kwara daya ba zasu baka dama ka sake creating wani
ba har sai kayi subscription da su saboda su services nasu ba kyauta bane. Zaka
rika biyansu akalla dala 8 duk wata kuma basa accepting subscription na wata
daya, karanci shekara daya ne. kaga kenan zaka yi lissafin dala takwas sau 12
sune adadin kudin da zaka biya su don more amfani da portal nasu.
AMFANINSU
§
Suna da matukar saukin sha’ani.
§
Zaka iya amfani da emails daban-daban don sake
register don more garabasar app daya da suke bayarwa.
§
Shi app dayan zaka iya updating dinsa ta hanyar
cire content dinsa kacokan ka sanya wani content din.
§
Apk dinsu is highly compressed basu cika nauyi
ba.
§
Apps dinsu yana da cpc mai kyau.
ILLOLINSU
§
Idan baka yi subscription da su ba, to ba zasu
baka damar sanya admob ad units dinka ba.
§
Basa karbar subscription na wata daya sai akalla
ya kai na shekara.
§
Suna sanya watermark a free apps dinsu, wato
alamar cewa a wajen su ne kayi app din.
§
Idan subscription dinka na dala 8 ne a wata to
ba zaka iya customizing package name naka yadda kake so ba.
Shiga nan don jarabawa ANDROMO
2-
APPSGEYSER: su kuma appsgeyser shima portal ne
da ake hada apps wanda a tunani na shine yafi kowane portal saukin sha’ani sai
dai shi apps din da zaka iya kirkira da su yan kadan ne gaskiya. Su already
akwai template na apps din kawai zaka canja suna ne, da icon sai wasu yan
kananan abubuwa wadanda ba’a rasa ba. Apps din da zaka iya yi da su, sun hada
da chat app, browser, ebook reader da sauransu. Su Appsgeyser zasu baka dama ka
sanya admob ad unit dinka a apps dinka sai dai zasu rika nuna 50% ads naka 50%
ads nasu.
AMFANINSU
§
Saukin sha’ani don har sun fi andromo sauki.
§
Suna baka damar monetizing app naka.
§
Zaka iya publishing app nasu a playstore.
ILLOLINSU
§
Ba kowane app ake iya hadawa da su ba.
§
Suna sanya ads dinsu a cikin app naka.
§
Apps dinsu suna da dan nauyi.
§
Ads dinsu iya interstitial ads kawai yake nunawa
baya nuna banner ko reward video.
Shiga nan don jarabawa
3-
APPYPIE: shima wani portal ne wanda ake creating
android apps ko iphone kai har ma da Windows apps su kuma usually suna baka
tsawon sati biyu ne ka jaraba amfani dasu a kyauta wanda bayan sati biyun nan
ya wuce to ba zaka iya cigaba da amfani da su ba har sai kayi subscription. Gaskiya
suna da features masu kyau, zaka iya yin apps masu kyau sama da kala dari masu
ban sha’awa.
AMFANINSU
§
Suna features masu kyau don features dinsu yafi
na andromo kyau.
§
Suna supporting different apps kamar irin su
website apps, ebook, notebooks da sauransu.
§
Zaka iya publishing na apps dinsu a playstore.
§
Suna da push notification feature wanda zaka iya
tura ma duk wanda yayi installing na app dinka message. Wannan feature din sune
kadai suke das hi a duk cikin portals da muka lissafa.
ILLOLINSU
§
Suna da yar wuyar sha’ani ga dan koyo ba kamar
appsgeysa da andromo ba.
§
Site dinsu is not mobile friendly, ma’ana idan ba
da PC kake using ba to gaskiya zai rika yi maka slow ne
Ku shiga nan don jarabawa APPSGEYSER
4-
APPYBUILDER: appybuilder ma wani portal ne da
ake amfani da shi wajen hada app wanda zaka iya kusan duk wani app da ka sani
ta hanyar amfani da shi. Appybuilder da duk sauran portals ire-iren shi ana kiran su drag
and drop portals saboda su zaka rika dragging and dropping na feature ne kawai
daga baya sai kayi compiling.
Appybuilder ya sha bambam da duka sauran portals din da muka ambata tun daga
tsari da yanayi da kuma yanayin aiki. Sannan shi appybuilder kyauta ne ake
amfani da shi zaka iya monetizing app din ka fully ta hanyar nuna banner da
interstitial ads a app dinka kuma zaka iya customizing package name na app
dinka yadda kake so.
AMFANINSU
§
Kyauta ne gaba daya babu wani subscription.
§
Zaka iya importing na wani feature wanda basu da
shi ta hanyar amfani da extension files.
§
Zaka iya amfani da souce code kawai kayi editing
ka sanya details naka.
§
Zaka iya publishing app dinka a playstore.
§
Suna da saukin sha’ani musamman idan apps din ka
masu saukin building ne.
ILLOLINSU
§
Duk earning din ka na google suna da 5% shi yasa
ba zaka iya using dinsu ba dole sai da gmail.
§
Idan kana bukatar extension to ba duka bane suke
bayarwa free dole ka saya akan kudi mafi karanci dala 10.
§
Suna da low cpc.
§
Wasu apps dinsu google basa yarda ayi publishing
dinsu a playstore misali earning apps.
Shiga nan don jarabawa APPYBUILDER
5-
KODULAR CREATOR: kodular creator shima kamar
appybuilder ne saboda shima yana cikin family din drag and drop ne, idan ka iya
appybuilder baka da bukatar koyon kodular haka kuma idan ka iya kodular baka da
bukatar koyon appybuilder . kusan komai nasu daya ne, sai dai extension ko
source code na kodular baya yi a appybuilder hakanan kuma na appybuilder baya
yi a kodular kuma ba zaka iya bambancewa ba saboda duka source codes dinsu yana
karewa da .aia ne, haka kuma duka extension nasu yana karewa da .aix ne don
haka duk wanda ya baka extension ko ka saya to dole ya gaya maka na wane portal
ne, saboda idan kayi uploading zai hau portal din amma ba zai yi ba kuma ba zai
ce maka wai ba nasa bane ba.
Amfanin kodular da appybuilder kusan duk
daya ne, dan bambancin shine kodular yafi dadin sha’ani ga wanda ya fahimce
shi, amma appy builder yafi sauki ga dan koyo. Abu na biyu kodular sun fi
appybuilder cpc mai kyau. Abu na uku su kodular ba’a iya hada earning app da su
wato application wanda baya containing komai sai ads. Shi yasa idan ka kammala
app da su to tilas sai kayi requesting for review sun tantance sannan ya fara nuna
ads.
Sannan kuma suna da wata illa daya bayan ka
gama building apps dinka to tilas ka saurara minimum of 48 hours sannan kayi
requesting review amma idan publishing zaka yi a playstore to ba sai jira ba,
kawai kayi publishing duk da baya nuna ads din, da zaran ya shiga playstore zai
fara nunawa.
Domin jarabawa shiga nan KODULAR
Anan zan tsaya sai kuma nan gaba idan na
samu time zamu yi video na yadda ake hada apps din a wasu daga cikin portals
din da nayi bayani.
KARIN BAYANI 2349034836666 whatsapp only
