Kamfanin Etisalat wadanda suka canza suna zuwa 9Mobile kwanakin baya sun kawo wata sabuwar garabasa ga abokan huddar su. Wanda zai baka damar kallon kowane irin video daga rumbun videos na YouTube kyauta ba tare da sun caje ka ko sisin kwabo ba. Hakanan kuma zaka iya kallon video, ba tare da kana da kudi a Layin ka ba, wato ko da account din ka 0.00 yake, wannan ba zai hana ka samun damar more wannan garabasa ba.
Sai dai kuma fa da sharadi kamar haka:
Sharadi daya ne shine ka yi subscription na monthly data bundle da kudin ka, su kuma zasu baka damar bude kowane irin videos ba tare da jan data din ka ba, tun daga karfe daya na dare har zuwa karfe biyar na asubahi. Ma'ana 1am zuwa 5am kenan.
A LURA
Idan ka shiga YouTube kafin karfe daya na dare ko bayan karfe biyar na asuba to zasu sambadi data din ka ne...
Wannan tsarin zai taimaka musamman ga mutanen da ke kallon film online da kuma wadanda suke kasa bacci da daddare.
Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.