-->

Monday, 11 December 2017

MENENE PHONE REPLICATION KUMA YAYA AKE YIN SA?

Phone replication ko phone cloning wani feature ne dake baka damar kwafe duk wasu files, da settings da tsari na wata waya zuwa wata waya cikin ƙaramin lokaci. Shi wannan feature din Xender ce take zuwa da shi koda yake akwai wasu softwares din da aka kirkira don replication din kawai. Kusan kowa ya san Xender amma ba kowane ya san cewa tana zuwa da phone replication feature baKusan duk wanda zai rabu da waya babban abinda yafi zullumi shine files dinsa irinsu videos, audios, pictures, settings, ring tones, wallpapers, Screensavers da sauran su.



MISALI
Kana amfani da waya, bayan ka loda mata files naka sai ka canja wata, to anan zaka iya kwashe duk kayanka ka maida su akan sabuwar wayar tun daga music, videos, messages, contacts, notes Kai har settings dinka.

YADDA AKE PHONE REPLICATION DA XENDER
◀▶Da farko ka tabbata dukkan wayoyin biyu anyi installing Xender a cikin su.
◀▶Daga nan sai kayi launching Xender da duk wayoyin, ma'ana ka bude xender application.
◀▶Bayan ka bude Xender sai kayi clicking akan dan circle (xender DP) din nan dake can saman screen daga gefen hannunka na hagu.
◀▶Zata nuna maka options kamar haka:
Ranking
More
Connect to PC
Phone replicate
Da sauran su

◀▶Sai kayi clicking phone replicate
◀▶Zata baka option biyu kamar haka "OLD" "NEW"
◀▶Wayar da kake son kwafar files din cikinta sai kayi clicking "OLD" nan take zata fara searching sabuwar.
◀▶Wayar kuma da kake son loda ma kayan sai kayi clicking "NEW"
◀▶Nan take sabuwar wayar zata tambaye ka kamar haka:
Old phone is an android
Old phone is an iPhone
◀▶Sai ka zaba idan tsohuwar wayar Android android ce ko iPhone.
◀▶Da zaran ka zabi operating system dinka nan take zata kai ka feji na gaba, inda zata tambaye ka shin waccan sabuwar wayar ma tana dauke da Xender? Karka bata lokaci anan tunda kana da Xender already har kayi launching ma, kawai kayi clicking akan next.
◀▶Kana yin clicking akan next zaka ga ta sanya maka wata alama kamar kayi creating (send) zaka tura wani abu.
◀▶Daga nan sai ka koma kan tsohuwar wayar ka wadda ke searching sabuwar wayar already. Anan take zasu yi connecting da junansu, sai tsohuwar ta fara antaya ma sabuwar dukkan kayan da suke a cikin ta.

Da zaran sun kammala zaka ga sabuwar wayar tana dauke da dukkan abinda waccan tsohuwar take dauke da shi, irin su settings, wallpapers, applications, music, videos da sauran su.

NOTE
Wannan bayanin baki daya an yi shi akan xender ne, don haka ban ce yana yi da gionee xender ko senderit ba. Ehe

Wannan shi ake kira phone replication.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

Copyright (sirrinwaya 2017)

NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner