-->

Saturday, 30 December 2017

YADDA ZAKA KOYI COMPUTER DAGA KAMFANIN GOLDEN BRAIN COMPUTERS A KYAUTA

Shahararren kamfanin nan mai suna Gonden Brain Hub ICT sun yi namijin kokari wajen gabatar mana da free computer training. Training ɗin zai kasance ne in a MOOC (Massive Open Online Course) format wato komai online za'a yi shi. A takaice dai zaka iya gwanancewa da sarrafa computer alhali kana daga dakinka kwance cikin kwana talatin kacal.



Babban abin burgewa duk wannan namijin kokari da suka bijiro da shi basa cajin ko sisin kwabo, duk kyauta ne. Sanin kowane cewa yanzu amfani da Computer ya zama ruwan dare har ma wasu ma'aikatu basa kula daukar ma'aikaci matukar ba computer literate bane. Kenan wannan is a golden opportunity for all of us to learn computer appreciation cikin ruwan sanyi.

Ga wanda yake da sha'awa sai ya shiga nan yayi register. A yayin register din ana bukatar email address wanda yake aiki domin zasu tura maka congratulatory message. Daga nan sai ka zarce email inbox dinka kai tsaye, inda anan zaka samu message din su a inbox dinka. Kawai ka bude message din kayi scrolling can kasa zaka ga an rubuta click on me to start learning da blue din rubutu sai kawai kayi clicking. Nan take zai kai ka ajin da zaka fara koyon darussan.

Darussan sun raba su zuwa gida biyar sune kamar haka:

⚫ CS 101: General computing
⚫ CS 102:  Microsoft Word
⚫ CS 103:  Microsoft Excel
⚫ CS 104:  Microsoft PowerPoint
⚫ CS 105:  Internet Basics

A karkashin kowane course sun rarraba shi page by page don saukaka harkar koyo da koyarwa.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

© Copyright (sirrinwaya 2017)
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner