-->

Thursday, 26 October 2017

YADDA ZAKA RIKA AIKA SAKON TEXT KYAUTA KOMAI YAWAN SA

Kwanakin baya da dadewa mun yi alkawarin kawo maku hanya mafi sauki da zaku rika amfani da ita wajen tura sakon kar ta kwana wato text message ko kuma SMS a kyauta zuwa kowane layi. Wato ko MTN ko Etisalat ko Airtel ko Glo kai har ma da wayoyi kirar CDMA kamar su Multilinks, Starcoms, Reltel, Visafone da sauran su. Komai sai Allah ya nufa a lokacin da muka yi alkawarin bamu samu damar yin rubutun ba, to Alhamdulillahi yau Allah ya amince.


Ba tare da wani bata lokaci ba, idan kana bukatar tura sakon kar ta kwana a kyauta ka shiga nan shiga nan kai tsaye. Zasu baka wasu culums kamar haka :

1- MOBILE NUMBER
Anan suna bukatar number din zaka yi ma message din ne kuma ana bukatar number din in international format ma'ana ta fara da +234 sai dai kuma su da kan su automatically zasu sanya maka +234 kai kuma sai ka karasa. A takaice dai idan ka tashi sanya number din karka sanya zero din farko. Kenan idan number din da zaka tura message mai 080 to ka cire zero din farko sai ka sanya 8012345566 ko kuma idan mai 070 ne zai kama 70.... Ko kuma 81....

Ka kula duk kayi kuskure wajen sanya number to message din ka babu inda zaya je.

MESSAGE
Colum na biyu kuma anan ne zaka rubuta message din ka. amma a yi hattara kar ka yi amfani da kalmomin da yan damfara suka cika amfani da su kamar irin su "congratulations" ko "You have won" ko "account credited" da sauran su. Da zaran ka sanya dayan wadannan kalmomi to automatically zasu yi blocking messages din ka.

Ka'ida ta biyu kar message din ka ya wuce 160 characters, lokacin da kake rubuta text din zaka ga suna kidaya maka ko characters nawa ka rubuta da kuma yawan characters din da suka rage maka. Idan ka wuce ka'idar character limit nasu to message din ka ba zai je ba.

Abu na gaba kuma na karshe a karkashin colum na biyu shine ka tabbatar number din da kake turawa message bata bisa tsarin DND. (Domin kana bisa tsarin ko kuwa a'a tura sakon help zuwa 2442)

VERIFICATION CODE
Anan zasu baka wasu numbers daga gefen Colum din, to su ake so ka kwafa a cikin culum din sannan sai kayi scrolling down zaka ga "SEND" sai kayi clicking dinsa nan take wanda ka tura ma message din zai ga message din a wayar sa.

Ka sani message din ba zai shiga da lambar wanda ya turo ba zai shiga da sunan portal din SMS din ne wato "SMS BOX". Saboda haka ni shawarar da zan baka ka tabbatar wajen tura message din ka rubuta sunan ka ta yadda wanda ka tura ma message din zai gane ka cikin ruwan sanyi.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner