-->

Wednesday, 26 October 2016

APPLICATIONS GOMA DA YA ZAMA DOLE DUK DALIBI YA MALLAKA

Sayen wayar Android ba tare da ka fimfa ta softwares ba o boy you are just wasting your money. Akwai wasu applications da ya zama dole ga wadanda ke rike da wayoyin Android su mallaka musamman ma dalibai iri na. Zan lissafa goma daga ciki idan kuna da kari ku kara mana.

 1- English
 Dictionary ne wanda bana tunanin akwai wani dictionary a gaban sa a duk fadin Google play store.

 2- Camscanner
 Application ne dake baka damar converting duk wani littafi zuwa ebook. Zaka iya aro littafi kayi converting din shi zuwa soft copy ta hanyar amfani da Camscanner 

3- Calculator
 Dole ne dalibi ya mallaki calculator a wayar sa saboda tsaro.

 4- Notebook
 Application ne da ke baka damar pasting duk abinda kayi copying kayi saving din shi a wayar ka komai yawan sa. Sannan kana iya printing din shi duk sa'adda kake bukata.

 5- Letter Writing
 Application ne dake kunshe da duk sample din letter writing kama daga job application letter, resignation letter, acceptance letter, suggestion letter, cover letter and many more.

 6- Okada Book
 Application ne mai qunshe da dubunnan litattafai na Hausa da na turanci. Kuma kaima zaka iya wallafa littafi kayi uploading ka cigaba da karbar kudi kana gida kwanciyar ka.

 7- Adobe Reader
 Shine ke baka damar bude PDF files wato ebook

 8- WPS Office
 Zaka iya creating ebook da shi naka na kanka

 9- Google Translator
 Zaka iya fassara duk wani yaren da baka fahimta zuwa wanda kake fahimta. Misali turanci zuwa Hausa ko Hausa zuwa Yoruba ko Igbo zuwa Larabci ko French zuwa Swahili.

 10- English Grammar
 Zai taimaka maka wajen ganin ka gyara turancin ka. Wato dai ka zama ko a gaban Hillary Clinton kayi turanci to sai ta tafa maka. Duk apps din da na lissafa akwai su a Google play store ka shiga kayi searching kawai. Wadannan kadan kenan daga application 10 ga dalibai. Saura application goma da suka zama dole ga yan kasuwa
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner