-->

Friday, 21 October 2016

YADDA ZAKA RIKA BROWSING A KYAUTA DA LAYIN AIRTEL

Wannan ba cheat bane ba kuma trick bane sabuwar hanya ce da kamfanin Airtel tare da hadin guiwar Mark Zuckerberg suka kirkira don ba ma yan Nijeriya damar shiga Internet koda basu da sisin kwabo.

Sai dai fa ba kowane website ne zaka iya shiga kyauta ba akwai iyakar websites din da suka bada damar shiga don haka duk wani website ba wadannan ba to ba zaka iya samun damar shigar su ba.

Websites din kyautar sun hada da

1- Facebook
2- BBC
3- Naij
4- Nairaland
5- Messenger
6- Goal.com
7- Arewa Lyrics
8- Wikipedia
9- Dictionary.com
10- Wiki how

Da sauran su

Don morewa shiga Google play store kayi searching "free basics" kayi downloading kayi installing kayi launching zaka ga duk websites din da na lissafa maka har da wasu ma.

Wanda baya bukatar downloading na application din sai ka shiga browser din ka kawai ka sanya wannan address din 0.freebasics.com nan take zai kai ka dukkan websites din da na gaya maka.

KARIN BAYANI
Idan da browser zaka yi amfani kar kayi amfani da UC browser don bata yi sai dai kayi amfani da Opera ko Chrome ko default browser din ka.
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner