Bayan da kamfanin sadarwa na MTN ya kirkiri sabon tsarin Instagram data bundle da aka fi sani da suna MTN Instabinge, kamfanin sadarwa na Airtel ma ba'a bar su a baya ba, don kuwa yanzu haka sun yi yunkurin bullowa da sabon tsarin su na Instagram bundle, wanda ke baka damar samun 1GB akan kudi ₦200 kacal.
Kowa yasan yadda Instagram yake sassambaɗar data kamar babu gobe, saboda kasancewarsa masuburbuɗar sharing hotuna da videos masu cikakken quality. Wannan ne babban dalilin samar da Instagram bundle don saukaka ma masu amfani da shi wajen sanƙame data babu ƙaƙƙautawa.
YADDA ABIN YAKE
Zaka yi recharging ₦200 sai ka danna *141*205# kayi activating. Da zaran ka danna wadannan lambobin zasu fece da ₦200 su antayo maka 1GB.
Babban amfaninsa shine zai saukaka maka barnar data din da Instagram ke sambaɗe maka, sannan kuma yana aiki akan both 3G ko 4G network, illar shi shine validity dinsa iya awa ashirin da hudu ne kacal zai yi expire.