-->

Tuesday, 18 December 2018

YADDA ZAKA FARA KASUWANCIN SAYAR DA DATA WATO DATA RESELLING



Kasuwancin data reselling shine kasuwancin saro data mai yawa daga kamfanonin sadarwa irinsu MTN, Glo, 9mobile ko Airtel kai kuma sai ka rika turawa mutane tamkar dai yadda ake sayar da katin VTU.

Kasuwancin data reselling ba sabon kasuwanci bane. An dade ana yinsa, shi yasa naga ya dace in dan yi bayanin yadda ake yin ta watakila akwai mai sha'awar yin ta amma bai san yadda zai fara ba. To da farko dai zanyi magana akan hanyoyi guda biyu wadanda da su ne ake amfani wajen fara kasuwar.

1- Zaka iya saro data din daga kamfanonin sadarwa kai tsaye, sai dai wannan sai kana da akalla jarin dubu biyar (5000) kuma zaka ga ribar qurarra ce. Ma'ana babu yawa sosai saboda baka sanya kudi da yawa ba. A takaice dai su a wajen su yawan jarinka yawan ribarka.


Advantages din saye directly wajen MTN sune:



A- Zaka iya amfani da kowace irin waya komai karantar ta wajen fara kasuwancin. Kai koda Nokia torchlight zaka iya amfani da ita.
B- Kaine zaka rika tura data din directly zuwa lambar kwastomanka.
C- Zaka loda katin kudin da zaka sayi data din a wayarka ne.
D- Harkallar tsakanin ka da MTN ne, don haka idan ka samu matsala zaka kira MTN ne   ko kuma kaje ofishin su don su gyara maka.


DISADVANTAGES DIN SARI DAGA MTN

A- Ga mai ƙaramin jari babu riba sosai.
B- Ga wanda baya da yawan customers masu saye akai-akai, akwai yiwuwar ka rungumi gwari
C- Idan data din MTN ka yi oda to iya data din MTN kawai zaka iya sayarwa banda sauran networks.
D- Baka
Wannan kenan a takaice



2- Hanya ta biyu kuma zaka iya sarowa daga third party data reselling company, wanda a gaskiya ga mai ƙaramin jari yafi sauki kuma yafi riba. Advantages din saya wajen third parties sune:

A- MTN 1GB da ake sayar maka 600, 700 har 800 zasu sayar maka da shi akan 470.
B- Zaka iya kasuwancin VTU dasu, inda zasu rika cire maka 5% akan kowane kati. Kuma katin su normal VTU ne ba wai transfer ba (share and sell). Kaga kenan duk katin 100 da zaka sayar kana da ribar Naira 5, katin 200 ribar Naira 10.
C- Zaka iya farawa koda da dubu biyu ne
D- Zaka iya sayar da data din kowane kamfanin sadarwa

Disadvantages din saye wajen third-party companies
A- Dole sai da babbar waya akalla wadda zata iya browsing.
B- Dole kayi amfani da account na banki wajen funding wallet naka.
C- Ba kaine zaka rika tura data din directly zuwa ga kwastomominka ba, Idan wani ya sayi data a wurin ka zaka shiga website din kamfanin ka tura details na kwastoma, kamar lambar wayar da za'a tura ma data din, network din kwastoma, sai yawan data din da ake bukata. To anan su kuma sai su tura, wani lokaci idan request yayi masu yawa suna dan jinkiri kafin su tura.
D- Idan ka samu matsala dole sai dai ka kira su a waya, kiran su ba kyauta bane.

Da sauran su

Cigaba anan



NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner