-->

Thursday, 20 December 2018

YADDA ZAKA FARA KASUWANCIN SAYAR DA DATA WATO DATA RESELLING (CIGABA)


Wannan cigaba ne daga rubutun da na fara jiya, na kuma yi alkawarin cigaba a yau insha Allahu, wanda bai karanta rubutun farko ba ya shiga nan don jin farkon yadda abin yake kuma hakan zai sai ka gane shi kan shi wannan din.

Jiya nayi bayanin hanyoyin da ake sarin data da kuma advantage and disadvantages na kowane daga ciki, yau ba tare da bata lokaci ba zanyi bayanin yadda ake sayen data din kai tsaye.



YADDA AKE SAYEN DATA DAGA MTN
Da farko bayan ka bibiyi duk bayanan mu ka yanke shawarar inda zaka sayi data dinka, to dole sai ka shiga tsarin MTN SME tariff plan ta hanyar rubuta sakon text a tura zuwa 131. Bayan kayi nasarar canza tsari to sai ka loda akalla dubu 7500 sannan sai ka danna wadannan lambobin:

*461# sai ka dannan malatsin kira
Bayan gajeren loading menu zai bude maka.
Sai kayi reply da 2 wani menu din zai bude maka.

Anan sai ka zabi iya karfin jarinka, tunda 7500 ce kayi recharging sai ka zabi option na daya, ta hanyar reply da 1. Anan take zasu sheke 7500 din su antayo maka data mai karfin 10GB. Kenan duk idan ka sayar da data din akan 500 a duk gig daya zaka tashi da ribar 2500.

Yanzu ka sayi data saura fara sharing ma customers din ka... Shima sharing din the same process zaka bi, sai dai wannan lokacin zaka zabi lamba ta shida ne wato share SME, sai ka bi umarnin da menu din ya baka.


YADDA ZAKA SARI DATA DAGA THIRD-PARTY COMPANIES

Da farko dai kamar yadda na fada dole sai kana da waya mai browsing, zaka yi amfani da ita wajen shiga. Bayan ka tanadi waya mai browsing kuma da data sai shiga browser dinka. Sai ka sanya wannan address dinhttp://www.clubkonnect.com a address bar naka Shafin farko zai bude maka, sai kayi clicking akan register, wani shafin zai bude maka, inda zaka rubuta cike sunanka, sunan mahaifi, lambar waya, email address da sauran su.


Bayan register, sai kayi login da lambar wayar da kayi register da ita da kuma password din da ka zaba...

Daga nan zai bude maka shafin farko, zaka ga wallet dinka is empty ma'ana 0.00 Sai kayi clicking akan deposit money. Shafi zai bude maka inda zasu tambaye ka adadin kudin da zaka yi depositing a wallet naka. Sai ka zabi payment method. Ga mai karamin karfi zai zabi payment through ATM card ne....

Ka sani ko nawa ka sanya a wallet dinka kamfanin interswitch (quickteller) zai sanqame kashi daya da ɗigo biyar bisa dari wato 1.5% na ladar wahalar tura kudi da yayi maka. Kenan cikin duk cikin Naira 100 suna da Naira daya da sule biyar, cikin Naira dubu suna da Naira sha biyar.

Bayan kayi depositing kudi successfully, sai ka koma home zaka ga adadin kudin da ka sanya a cikin wallet naka kamar haka




Daga nan ka kammala komai, duk lokacin da zaka tura data, zaka shiga account dinne kayi selecting buy data bundle. Wani shafi zai bude maka inda zaka sanya adadin data, ko 1gb ko 2gb ko wani abu mai kama da haka. Sai lambar wayar wanda zaka tura mawa, sai network dinsa. Shikenan sai kayi sending, cikin ƙaramin lokaci zasu tura ma client dinka data dinsa.

Ka lura wajen cike details na client naka ka tabbatar baka yi activating auto renewal ba, idan ka manta ka sanya shi active to da zaran data din kwastoman ka tayi expiring kuma kana da kudi a wallet dinka to zasu sake tura mashi data automatically su cire kudinsu a wallet naka.

Haka nan zaka iya sayar da katin VTU ta hanyar amfani da kudin da yake a wallet naka ko tura bulk SMS....

Wannan kenan a takaice, daga karshe ka sani third party data reselling companies suna da yawa na takaita akan clubkonnect.com ne kawai don bana son bayani yayi tsawo. Amma still idan baka gane ba ko kana bukatar karin bayani ka tuntube ni a whatsapp akan wannan lambar 09034836666. Please WhatsApp kadai kar ka kira ni
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner