-->

Sunday, 26 August 2018

YADDA ZAKA SAMU 50MB KYAUTA A LAYIN MTN


Koda yake wasu daga cikinku suna da labarin wannan garabasar, wasu ma ina da tabbacin sun dade suna sheqeta, amma duk da haka naga ya kamata na dan kara maku bayani akanta watakila wasu sun sani amma basu tabbatar tana aiki ba, wasu kuma watakila basu sani ba kwatakwata.

Anyway, a takaice dai wata sabuwar garabasa ce mtn ta kirkira don kara kankame kwastomominsu. Yadda tsarin yake shine zaka yi downloading na sabon application din mtn mai suna myMTN a google playstore ga wadanda suke amfani da android, ko kuma itunes store ga wadanda suke amfani da wayoyin iphone. Idan ka shiga compatible store naka sai kayi searching myMTN kayi downloading dinsa.
Bayan kayi downloading sai kayi installing kayi launching, a wajen country sai ka zabi sunan kasarku wato Nigeria ko kuma koma wace kasa kake, wajen sanya phone number sai ka sanya lambar wayarka. Daga nan zasu turo maka verification pin ta lambar da kayi register da ita. Sai kayi verifying, kana kammala verifying zasu sankamo maka data dinka ba tare bata lokaci ba.
Karin bayani, domin downloading din myMTN akalla kana da bukatar mb 20 saboda shi kanshi application din mb 15 ne.
Kada a manta 500 mb din da zasu baka validity dinshi kwana 3 ne, don haka ka natsu idan ma ka tsaya tattalinsa da yakai kwana uku ko baka cinye shiba zasu kwamushe kayansu ne.
Hakanan kuma zaka iya amfani da app din wajen yin abubuwa da yawa ba tare da kaje ofishin mtn ba. Ta hanyar amfani da app din zaka iya sayen katin waya ko data ma kanka ko waninka, zaka iya checking na ragowar airtime da data dinka. Zaka iya kuma monitoring yadda kake amfani da data dinka, zaka iya aika sakon sms kyauta, zaka iya reserving na lambar waya da sauransu.

For subscribe us or follow our facebook page Sirrin Waya
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner