-->

Sunday, 5 August 2018

KAMFANIN GOOGLE ZAI SAMAR DA FREE INTERNET A WASU JAHOHIN NIGERIA


Shahararren kamfanin nan na komai da ruwanka wanda aka fi sani da Google zai samar da free internet access a wasu jahohin Nigeria. Kamfanin yayi alkawarin harba free Wi-Fi wanda akalla mutum miliyan goma zasu amfana da shi.
Kamfanin ya bayyana cewa zai samar da service stations 200 a fadin jahohin Lagos, Kaduna Port Harcourt, Ibadan da kuma Abuja daga nan zuwa shekarar gobe wato 2019.
An bayyana kudirin ne a ranar Alhamis din da ta gabata a bikin Google for Nigeria da aka gudanar a jahar Lagos. Haka nan kuma kamfanin na Google ya bayyana karin tagomashi da suka yi ma wasu daga cikin manhajojinsu da suke kira da sunan go products suites ko kuma go series, wadanda suka hada da Google Go, YouTube Go, Google Maps Go and Android Go.

Da take tofa albarkacin bakinta director Google Nigeria Juliet Ehimuan-Chiazor ta bayyana cewa manufar kamfanin shine samar da saukin data da kuma reliable data ga mutane duba da yadda mutane suke fama da tsananin tsadar data subscription. Ta kuma bayyana cewa hanya a bude take wajen yin hadin gwiwa da sauran kamfanonin samar da signals na Nigeria.
A nata jawabin mataimakiyar shugaban Google products management Anjali Joshi tace, kudirin zai cigaba da yaduwa a sauran kasashen Africa.

Shi kuwa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana jin dadinsa game da kudirin tare da alkawarin cewa gwamnatin tarayya a shirye take wajen bayar da dukkan goyon bayan da ake bukata da cimma kudirin.
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner