-->

Monday, 29 January 2018

YADDA ZAKA BINCIKA MATSAYIN KATIN ZABEN KA


Zaben shekarar 2019 na matsowa kusa don haka na ga ya kamata a yi ma mutane bayanin yadda zasu bincika matsayin katin zaben su, shin ya zama ready ko kuwa a'a, shin zai iya zabe ko kuwa baya yi.



Dalilin wannan rubutun shine mu talakawa bamu da wani makamin kare dangi sai katin zaben mu, kuma da shi kadai ne zamu iya amfani wajen antaya ma bara-gurbin yan siyasa makami mai linzami.

Ga wadanda basu da katin zabe su shiga su binciko wurin da ake yin rajistar katin zabe mafi kusa da su. Ga wadanda suka yi amma bai fito ba ko wadanda suka yi amma ba su tabbatar ingancin shi ba su shiga nan su tabbatar.

Dalilin binciken shine bari ganin kana da katin zabe, matuƙar baka taba yin zabe da shi ba to abu ne mai saukin gaske ka je rumfar zaben ka a bincika babu sunan ka ko kuma card reader ya kasa tantance katin ka saboda wasu matsaloli. Amma ga wanda ya taba yin zabe da katin shi to baya da bukatar sake dubawa saboda already bio-data din sa tana INEC database.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC itace ta kirkira wannan hanyar tun watan Afrilun shekarar da ta gabata. An kirkira hanyar ne don bama yan kasa sanin matsayin katin zaben su tun kafin lokacin zabe.


YAYA AKE YI?
1- Shiga wannan address din  http://voterreg.inecnigeria.org
2- Ka sanya sunan mahaifinka tare lambobi bakwai na karshen VIN number din ka

Wadannan lambobin dake cikin wannan katin na sama na cikin jan gidan nan sune VIN number na katin ka.
3- Idan aka yi rashin sa'a ka manta da lambar VIN din ka still kana da zabi, zaka iya amfani da rana, kwanan wata da kuma shekarar da kayi shi.

Idan ka bincika ka gano cewa katin ka lafiya ƙalau yake to sai ka gode ma Allah idan kuwa aka yi rashin sa'a ya samu matsala to karka tsaya bata lokaci ka yi hanzarin garzayawa zuwa ofishin hukumar zabe mafi kusa da kai don ka sake register.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

© Copyright SirrinWaya 2018
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner