-->

Monday, 29 January 2018

HOTUNAN MAHAUKACIYAR DA AKA KONA BAYAN KAMATA DA SASSAN JIKIN MUTUM


Ranar Asabar din da ta gabata wadda tayi daidai da 27 ga watan Janairun shekarar 2018 aka kama wata mahaukaciya da sassan jikin mutum. Lamarin ya faru ne a jahar Delta inda ma'aikatan tsafta ke kokarin tsaftace gari wanda aka saba yi duk ranar Asabar din karshen kowane wata. Yayin da aiki ya kawo su daidai mahadar express a DSC wurin da rumfar mahaukaciyar take.



Ma'aikatan sun yi yunkurin tsaftace rumfar mahauciyar a yayin da ita kuma kekasa kasa cewa babu wanda zai shigar mata rumfa. Bayan an shafe dogon lokaci ana takaddama da mahaukaciyar wanda cecekucen mahauciyar da ma'aikatan tsaftar ya jawo hankalin mutane da dama.

A karshe aka yanke shawarar shiga rumfar mahaukaciyar karfi da yaji inda aka samu wani bokiti a rufe. Da budawa sai aka tarar da danyun sassan jikin mutane a ciki. Take mutanen dake wurin suka fusata suka yi mata dukan kawo wuka, har ta fita hayyacinta. Fusatattun matasan basu hakura ba sai da suka sanya taya da man fetur suka kona ta kurmus.



NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner