-->

Monday, 1 January 2018

MENENE SIM PORTING KUMA YAYA AKE YIN SA?

Sim porting wato hijira da layin waya, wata dama ce da Nigeria Telecommunication Commission (NCC) ta kirkira wadda ke baka damar yin hijira da layin ka daga wani network zuwa wani network ba tare da number din ka ta canza ba.

MISALI
Kana da layin glo wanda ka dade kana amfani da shi, mutane duk an san ka da layin. Daga baya sai kamfanin glo ya sanyo ka gaba yayi tayi maka sata babu gaira babu dalili ga shi kai kuma kana son lambar layin. To ka sani zaka iya hijira ka koma duk network da kake bukata a Nigeria kamar MTN, Etisalat, Airtel da sauran su ba tare da lambar ka ta canza ba. Kana da ikon komawa glo din ka daga baya matukar ka shafe wata uku a network da kayi hijira zuwa gare su. 

Sim porting ba bakon abu bane don akalla yafi shekara daya da rabi ana yin shi, na yanke shawarar kawo shi a yanzu saboda ganin cewa mutane da yawa basu san ana yin sa ba.

ABUBUWAN DA YA KAMATA KA TABBATAR KAFIN PORTING 

1- Da farko dai ka tabbatar kai ne kayi wa layin ka register, idan ba kaine kayi register ba, to kamfanin da zaka tsere daga wurin su ba zasu amince ba, sai su yi tsammanin wani ne yake son accessing layin ka ba tare da sanin ka ba. 
2- Ka tabbatar network din da kake son fecewa daga gare su basu bin ka bashi, saboda idan suna bin ka bashi ba zasu amince ka tsere musu da sisin kwabo ba. 
3- Ka tabbatar baka da kudi ko data akan layin saboda gudun asara, don idan kayi porting to layin ka zai koma 0.00 ne.
4- Ka tabbatar ka kwashe duk wani important abu daga layin tun daga lambobin waya har zuwa messages.
5- Ka tabbatar kana da ID card don da shi ne za'a yi comparing su gani idan sunan da yake a jikin register din ka da wanda yake a jikin ID card dinka sun yi corresponding, shi yasa nace ka tabbatar kai ne kayi ma layin register.

Idan ka hada duk abubuwan da na lissafa a sama sai kawai ka tafi ofishin network din da kake son komawa, ka bayyana masu kazo porting ne zasu baka wani form wanda zaka cike duk details din da ka bayar a lokacin register. Idan ma baka iya cike form din zasu cika maka sai su tura ma network din da kake son fecewa request cewa mai wannan details din yana son barin network din ku zuwa namu. Su kuma zasu yi masu reply cewa eh basa bin ka bashi kuma details da ka bayar daidai ne.
 Don haka sai su yi comfirming hijirar ka.

Daga nan su kuma wadanda zasu karbe ka zasu baka sabon layin su, sai dai zaka ga baya dauke da lamba saboda kana da lambar ka already. Zasu ce maka da zaran ka ga network din wayar ka ya dauke to ka cire layin ka sanya nasu. Watakila kafin ka rufe baki ma zaka ga wayar ka ta sanya maka sim registration failed. Karka damu kawai cire layin ka sanya sabon kayi flashing tsohuwar lambar ka zaka ji ringing din ta ma ya canja ya koma na sabon network din da ka dawo.

Daga wannan rana kayi hijira, don haka da recharge card da data da checking balance duk zaka cigaba da amfani da sabon network din ka ne.

KARIN BAYANI
Ba zaka iya yin porting sau biyu a cikin abinda bai fi wata uku ba, duk bayan wata uku zaka iya komawa kuma wani network din, hakanan kuma zaka iya komawa network dinka na da idan kana bukata.

Abu na gaba porting kyauta ne ba'a karbar ko sisin kwabon ka, duk wanda ya caje ka sisin kwabo kayi reporting din shi directly to NCC ta hanyar kiran 622 daga kowane layi. Shima kiran NCC din kyauta ne.


Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

© Copyright (sirrinwaya 2018)
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner