-->

Tuesday, 2 January 2018

YADDA ZAKA SAMU CERTIFICATE DAGA KAMFANIN GOOGLE

Sama da wata shida da suka wuce kamfanin Google yayi alkawarin training ɗin yan Nigeria miliyan daya akan digital marketing wanda zai warware maka zare da abawa akan yadda ake kasuwanci online wanda har yanzu mutanen mu basu waye da shi dari bisa dari ba. A cikin training ɗin kamfanin zai yaye maka sirrin yadda ake fara kasuwa online komai karantar ta ko dai ta hanyar website, social media, email da sauran su. 
Yanzu haka an fara training ɗin kuma training ɗin kyauta ne, dadin dadawa ma har certificate zasu baka na shaidar kammala darasin. 

Abin alfahari ne ka mallaki certificate daga kamfanin Google musamman idan ka sanya shi a curriculum vitae (CV) naka, duba da irin kasar da muke rayuwa wadda a yau duk kwarewar ka akan abu matukar baka da certificate akan abin to a banza, haka kuma duk jahilcin ka akan abu matukar kana da shaidar iyawa to kai ne gwani.

Training ɗin dai ba wata wahala ce da shi ba don babu abinda ake bukata daga wurin ka daga Gmail sai data. Wanda baya da Gmail ya shiga nan ya bude sabo. Bayan ka bude Gmail sai ka shiga nan  ka yi login. Da zaran ka shiga to anan take ma zaka iya fara darasin. Sannan zaka iya farawa ka bari wani lokaci ka cigaba.
Darasin yana da module ashirin da uku, a karkashin kowane module  akwai sessions daban daban, a takaice dai zaka yi session tamanin da wani abu. A karshen kowane session akwai activity wata yar assessment test ce mai sauki wadda zata tambaye ka akan abinda ka karanta idan ka amsa zata wuce da kai session na gaba har ka kammala.

Duk module din da ka gama zasu baka badge wato alamar ka kammala wannan module din. Bayan kammala duka modules din zaka yi final exams wadda dukan ta objectives questions ne, sai dai kayi hattara ita final exams din ka ta sha bambam da activity da kayi a baya saboda ita activity zaka iya attempting sama da goma ita kuwa final exams attempt uku kadai gareka. Sai dai dadin ta duk idan ka fadi zasu nuna maka question din da ka amsa daidai da wadanda kayi kuskure sai ka sake attempting.

SHAWARA 
Kowane session yana da video da manuscript wanda ake bukatar ka karanta ko kuma ka kalla, shi manuscript din text ne lecture din ka, shi kuma video din lecture din ce abinda yake a manuscript shine cikin video din, don haka ina baka shawara da ka rika karanta text din maimakon playing video din. Saboda video din HD video ce idan data dinka ba mai kwarin gaske bace to cikin ƙaramin lokaci zata lashe. Shi kuwa manuscript ko Twitter bata kai shi tattalin data ba. 

Yanzu haka na kammala nawa har nayi downloading certificate dina kuma har nayi printing nayi laminating nayi updating CV dina.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.


Wasu daga muhimman rubuce-rubucen mu
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner