A yau ne 1 ga watan Janairun shekarar 2018, wannan yasa kamfanin sadarwa na Airtel suka yunkuro don faranta ma abokan huddar su rai, tare da taya su murnar shigowar sabuwar shekarar 2018. Airtel na bayar da kyautar data mabambanciya don haka sai wadda Allah ya ciyar da kai.
Ga codes din da zaka yi dialing don neman taka datar.
*141*13*200#
Idan kayi sa'a zasu baka MB 200
*141*13*100#
Suna bayar da MB 100
*141*13*50#
Don samun MB 50
*141*13*1#
Idan baka yi dace ba zasu baka MB 1
KARIN BAYANI
Ba kowane layi suke bamawa ba, saboda haka idan ka jaraba basu baka koda MB daya ba, kayi hakuri watakila zasu baka wata offer din a gaba.
Haka kuma kamfanin na Airtel har wa yau yayi alkawarin bama duk wani abokin huddar su da layin shi yayi wata uku ba cikin waya ba damar more ninki ashirin na duk abinda yayi recharging.
MISALI
Kana da Layin da yake a kasa na tsawon wata uku to idan ka dauko shi ka sanya a wayar ka sannan ka sanya ma shi Naira 100 to zasu baka Naira 2000, idan kuma ka sanya 200 zasu baka 4000 kuma kudin zaka iya amfani da su wajen kiran kowane layi, browsing kowane website ko downloading kowane irin file.
MORE NINKI GOMA NA DUK KUDIN DA KAYI RECHARGING DA AIRTEL SMART RECHARGE OFFER
Shi kuma wani tsari ne wanda kowa ma zai iya amfana da lagwadar shi wato tsofaffi da sababbin customers.
YADDA AKE YI
Idan zaka yi recharging na layin ka na Airtel sai kayi amfani da code din *220* recharge pin sai # maimakon *126*pin#. Duk idan ka sanya katin Naira 100 to zasu baka 250 ta kiran kowane layi, 750 ta browsing kowane website, ko downloading kowane irin file
Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.
© Copyright (sirrinwaya 2018)

