-->

Monday, 25 September 2017

SIRRIKA GOMA GAME DA SHAFIN YOUTUBE 1

Daya daga cikin manyan rumbunan videos kuma mafi shaharar su shi ne rumbun videos na YouTube. Mutane da yawa suna shiga YouTube su kalli finafinan Hausa, India, Chinese, Nigerian films da sauran su, sai dai kuma da yawan mutane basu san wasu sirrika boyayyi game da shafin na YouTube ba.

A yau muna dauke da sabon Post wanda zai yi tsokaci game da wasu boyayyin (hidden features) abubuwan da mafi yawan mu bamu sani ba. Ba tare da bata lokaci ba kai tsaye za mu fara abinda ya kawo mu.

YADDA ZAKA FITAR DA HOTO MAI MOTSI (ANIMATION IMAGE WATO GIF FORMAT)


Eh zaka iya cire dan guntun video mai tsawon kamar second biyu zuwa uku. Wannan video ana lissafa shi cikin hotuna ne kasancewar baya da sauti kuma baya da tsawon da za'a kira shi a matsayin video. Shi yasa ake kiran shi 'animation'.



Idan kana son ciro irin wannan hoton daga kowane irin video a you kawai shiga address na YouTube. Zabi video din da kake son ciro hoton daga cikin ta, idan ta bude sai ka shiga address bar na browser din ka wato wurin da kake sanya address na Website idan zaka yi browsing. Zaka ga address misalin haka http://www.youtube.com/watch?ghy1233
Sai ka kara kalmar 'gif' kafin YouTube din misali www.gifyoutube.com/watch?ghy1233
Nan take ba tare da bata lokaci ba zai tambaye ka cewa ka zabi daidai wurin da kake so ya ciro Maka sai kawai kayi clicking akan 'Create Gif'. Shikenan fa har ka kammala.

A dakace mu a rubutu na gaba don jin wani sabon sirrin.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.
Karanta 👉 CIKAKKEN DARASI AKAN YADDA ZAKA KIRKIRI ANDROID APPLICATION

NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner