Albirinku masoya layin Airtel, yanzu haka sun yunkuro sun kara kirkiro maku wani sabon tsari da ake kira da New SmartConnect ko kuma OverJara. Tsarin Airtel OverJara zai baka damar samun Naira dari takwas a duk lokacin da ka loda katin Naira dari kacal.
Kuma dadin dadawa za ka iya kiran kowane layi da wannan dari takwas din, zaka iya browsing kowane shafi haka kuma zaka iya tura sakon kar ta kwana duk a ciki.
Kamar yadda kamfanin na Airtel ya tabbatar, ya ce zaka iya more wannan garabasar ne kadai yayin da ka sayi sabon layin Airtel kayi register, ka kuma dora shi akan kowace irin waya including Nokia torchlight. Sannan kuma ba su tsaya anan ba, zasu rika tattara duk yawan recharging dinka na wata daya su rika tura maka a karshen kowane wata a matsayin kudin da zaka iya browsing kadai da su.
yadda abin yake shi ne idan ka sanya Naira dari a layin ka anan take yanke zasu sanya maka Naira darin ka a main account naka, sa'nnan su baka Naira dari biyu da hamsin wadda zaka iya kiran kowane network da ita. Ba za su rabu da kai haka ba, zasu kuma baka Naira dari wadda za ka iya kiran yan uwa da abokan arziki. Har wa yau zasu kara baka Naira dari wadda za ka iya browsing social networks kamar su whatsapp, Twitter, Facebook ko BBM idan ka hada a jimlace ka ga Naira dari daya tak ta jawo Naira dari takwas kenan.
Ina da tabbacin mutane da dama za su bakunci Airtel, mu kuma yan gida, sayen sabon layi ya wajaba akan mu.

