-->

Wednesday, 2 November 2016

YADDA ZAKA YI CONNECTING WAYAR KA DA MOUSE, KEYBOARD, JOYSTICK KO FLASH DRIVE

Kasan cewa idan kana da wayar Android zaka iya connecting dinta da wasu devices wadanda mu a iya namu ilimi computer ce kawai take supporting wadannan devices din?

To nesa tazo kusa domin yanzu zaka iya hada wayar da devices kamar haka:

1- Computer keyboard
2- Computer mouse
3- Game joystick
4- Android Phone
5- Flash drive
6- Internet Modem

Zaka iya more duk wadannan facilities ta hanyar amfani da OTG Cable wato On the Go Cable. OTG Cable kamar yadda kaga hoton shi a sama dan gajeren Cable ne da bai wuce inci 8 ba. Yana da edges (kawuna) guda biyu na farko kai ne irin na charger din Android the other one kuma USB port ne.

Idan kana son connecting wayar ka da duk wadancan devices din da muka lissafa sai kawai ka sanya OTG dinka a charging point na wayar ka sai ka jona duk device din da kake bukata a USB port din OTG din nan take wayar ka zata yi accepting duk abinda ka sanya mata kuma ka cigaba da controlling dinta da duk devices din da ka jona mata.

Idan ka jona ma wayar ka keyboard nan take zaka rika typing ta hanyar amfani da wannan external keyboard din da ka jona mata.

Idan kuwa mouse ka sanya mata zaka ga mouse cursor ya bayyana a wayar ka don haka baka da bukatar highlighting ko scrolling da wayar ka, sai kawai ka cigaba da amfani da mouse din tamkar computer.

In takaice maka dai koda wane irin device ka jona wayar ka dashi to hankali kwance zai rika functioning a wayar ka tamkar dai Computer.

KARIN BAYANI
Ka sani duk yawancin wayoyin da aka dade da yayin su basa supporting OTG cable. Kuma duk yawancin wayoyin da ake yi yanzu suna supporting din shi kai hasali ma suna fitowa da shi.

YAYA ZAKA GANE WAYAR DA KE SUPPORTING
A jikin kwalin ta zaka ga hoton kan USB cable dan karami.
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner