-->

Wednesday, 2 November 2016

YADDA ZAKA CI BASHIN DATA DA LAYIN GLO


Kamfanin glo ya kirkiro sabuwar hanya da take ba abokan huddar su damar rancen data yayin da subscription din su ya kare kuma basu da cikakken kudin sake subscription din.

Ta hanyar "Glo borrow me data" zaka iya cin bashin data up to 2GB ba zaka biya ba har sai sa'adda kayi recharging na gaba.

Dole ka tabbatar kayi akalla wata daya kana amfani da Layin kafin ka samu damar more garabasar.

Danna *321# sai kabi umarnin da menu dinka yayi displaying maka.

Haka kuma glo basu tsaya anan ba sun kirkiri wani sabon tsari da suka kira "Double free tomorrow". Shi kuma tsari ne da zai baka damar more ninkin duk abinda ka kashe wanshekare.

Misali
Sai ka kashe 100 ta hanyar kira, aika sakon text ko kuma ta hanyar hawa yanar gizo a yau to gobe zasu ninka 100 din nan da ka kashe su baka 200. Wani abin burgewa zaka iya kira, sakon text, hawa yanar gizo ko shiga dandalin sada zumunci.

Danna *300# don shiga tsarin.

NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner