-->

Thursday, 3 November 2016

YADDA ZAKA SAMMA ABOKIN KA CHAJI DA WAYAR ANDROID

Wani lokaci kana bukatar abokin ka ya turo ma wani abu amma baya da chaji, ko kuma wani lokaci kana da wayoyi guda biyu daya wadda kake daukar kira da wadda kake zagaye duniya (wato Internet browsing) sai aka yi rashin sa'a daya bata da chaji kuma kana da wani muhimmin kira da kake son yi ko kuma kana tsammanin wani muhimmin kira amma chajin ka ya kare.

To ga sabuwar hanyar da zaka iya amfani da wayar ka kirar Android ka charger wata wayar ko kuma ka tsotsi chajin wata wayar.

Ka samu OTG cable dinka (idan baka san menene OTG cable ba shiga nan) kayi connecting din wayar da kake son tsotse ma chaji da wadda kake son chajawa. Da zaran kayi connecting to wayar dake da karancin chaji zata soma zukar chajin yar uwarta.

KARIN BAYANI
Misali wayar da ake zukar chajin ta tana da chaji 80% to da zarar mai zukar chajin ta kai 60% to 70% automatically zata daina bada chajin. Don ba zata bayar da sadakar misalin chajin dake gare ta ba.

Kai in takaice maka akwai abubuwa da yawa wadanda ake yi da OTG cable da bazan iya bata lokacin rubutu akan su ba, kawai ka nemi OTG cable kai kanka zaka iya ganin wani abinda ban fada ba ma.
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner