Mutane da yawa suna kiran waya ta ko turo man message suna tambayar data subscription mafi sauki. Wannan yasa naga akwai bukatar in dan yi rubutu akan data subscription mai sauki.
Ba tare da bata lokaci ba ka shiga nan kayi register:
ABUBUWAN DA AKE BUKATA WAJEN REGISTER
1- Sunan ka
2- Sunan mahaifi
3- Email address
4- Lambar waya
5- Referral link (Sai ka sanya wadannan lambobin ck11542539)
Bayan ka kammala register sai kayi login zaka ga sun bude maka online wallet. Ita wallet din ka tamkar asusu ne a wurin ka domin kuwa zaka iya loda mata kudi a matsayin ajiya tamkar bank saving account. Sannan kuma da wallet dinka zaka iya sayen data ko airtime daga website din.
Kuma idan kana bukata a koda yaushe zaka iya transfer daga wallet dinka zuwa bank account dinka.
YADDA ZAKA SANYA KUDI A WALLET DINKA
Ka shiga website din wato http://www.clubkonnect.com kayi login da phone number dinka da password dinka. Zaka ga "deposit money" Sai kayi clicking akan sa. Sai ka zabi hanyar da kake son sanya kudin. Hanyoyin sanya kudin sune
1- ATM
2- Bank Transfer
3- Cash Deposit
4- Recharge card
Duk wanda ka zaba zasu gaya maka yadda zaka yi. Sai dai ka sani basa karbar kowane recharge card sai na MTN. Sannan kuma ka tabbatar da Layin da kayi register dasu da shine ka tura masu recharge card din. Kuma ko nawa ka sanya idan dai ta recharge card ne to zasu caje ka 150.
MISALI
Idan ka aika musu da recharge card din naira dubu to zaka ga sun sanya maka 850 a wallet dinka.
KARIN BAYANI
Da recharge card pin da transfer duk daya ne a wajen su don haka zaka iya sanya katin a wayarka ka samu bonus na recharging sannan ka tura masu ta hanyar transfer.
YADDA ZAKA SAYI DATA
Idan kana bukatar sayen data sai kayi clicking akan buy data. Zasu baka gidaje uku
1- Data network (wato network din da kake bukata, idan MTN ne sai ka zabi MTN)
2- Data value (yawan MB din da kake bukata)
3- Number (ka sanya lambar da kake bukatar MB din koda ba da ita kayi register ba.
Sai kawai kayi clicking akan send zasu turo maka data dinka cikin kankanen lokaci.
FARASHIN DATA DINSU
MTN
250MB = 200 NAIRA
500MB= 350 NAIRA
1GB= 550 NAIRA
ETISALAT
250MB = 250 NAIRA
500MB = 350 NAIRA
1GB = 650 NAIRA
Kowace data tana da validity na tsawon wata daya ne kuma tana budewa da kowace irin waya da kowane irin Application kai in takaice maka har da Computer yana aiki.
YADDA ZAKA SAYI AIRTIME
Bayan kayi login ka sanya kudi a wallet dinka sai kawai ka shiga buy airtime zasu baka columns uku kamar haka:
1- Airtime network
2- Airtime value
3- Number
Da zaran ka cike ka tura zaka ga sun turo maka katin ka in less than 3 minutes.
FARASHIN KATIN SU
Ko katin nawa ka saya idan ta VTU ne zasu yi maka saukin 5% (wato katin 100 suna sayar da shi 95 kenan) idan kuma ta share and sell ne wato transfer to zasu yi maka saukin 10% (wato katin 100 zasu sayar maka da shi akan naira 90 kenan.
Ka sani ta VTU ne kadai zaka iya samun duk bonus din da ake bayarwa amma idan ka zabi ta share and sell ne to ba zaka samu wani bonus ba.
GARGADI
Website din club konnect website ne na yan kasuwa baya da alaka ko ta sisin kwabo damu, don haka idan ka samu matsala da su ka kira customers care contact dinsu directly. Sannan kuma ka sani club konnect na iya karawa ko rage ma data ko airtime dinsu kudi don haka duk farashin da muka sanya to shine current price din su.

