-->

Wednesday, 19 October 2016

YADDA ZAKA RAGE MA VIDEO NAUYI

Kasan cewa akwai application na wayar Android wanda zaka iya rage ma VIDEO nauyi? Ma'ana ka tace shi. Misali kana da video a wayar ka kuma kana son video amma yayi occupying memory dinka, watakila ya kai misalin 250MB.

To karka yi saurin goge shi yanzu akwai sabuwar hanyar da zaka bi wajen ganin ka tace duk wani video mai nauyi a wayar ka. Video mai nauyin 250MB zaka iya maida shi 15MB cikin ruwan sanyi.


Kar in cika ku da surutu kawai shiga Google play store kayi searching "Video Compressor" ko kuma kayi downloading ta nan, da zaran kayi downloading sai kawai kayi installing kayi launching.

Da zaran ka bude shi zai nuna maka menu dauke da icons hudu.

Na farko Start
Na biyu My Videos
Na uku Rate
Na hudu More

Sai ka zabi na farkon wato start nan take zai kai ka cikin dukan videos din da ke kan wayar ka sai ka zabi video din da kake son tacewa kayi clicking akan ta. Anan zai kaika wurin da zaka zabi resolution din da kake bukata sai kawai ka taba "Compress" nan take zai tace maka video din ka.

Wanda ke da tambaya yayi
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner