-->

Monday, 29 July 2019

WHATSAPP ZAI ZAMA KISHIYAR PAYPAL, PAYONEER, GOOGLE PAY DSS

WhatsApp pay wani sabon tsarine da kamfanin manhajar sada zumunta ta WhatsApp zai kirkira. Tsarin na whatsapp pay zai ba masu amfani da WhatsApp damar karɓa ko tura kuɗi a duk fadin duniyar nan.

A takaice dai whatsapp zai zama kishiya ga PayPal, Google pay, Amazon pay, phonepe, payoneer da sauran payment portals na duniya. Kamfanin na whatsapp ya sha alwashin kaddamar da tsarin a cikin wannan shekarar a kasar India.

Kamfanin ya bayyana cewa masu amfani da manhajar zasu more tura kudi cikin ruwan sanyi tamkar yadda suke tura sakon whatsapp chat.
Kamfanin zai yi amfani da tsarin Unified Payments Interface (UPI) wanda zai taimaka ma masu amfani wajen karɓa da tura kudi cikin ruwan sanyi.

Kamfanin ya bayyana cewa, masu amfani da sabon tsarin zasu yi linking account dinsu na banki ne da WhatsApp. Hakan zai basu damar amfani da tsarin ta hanyar clicking akan payment icon wanda zai kasance kusa da camera icon na chat page. Da zaran kayi clicking payment icon, sunayen bankuna zai fito ka zabi bankin da kake son tura kuɗin.

Wannan tsarin tabbas zai share ma yan Nigeria hawayen su duba da yadda PayPal suke yi mana yanga da jan aji.

NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner