Hukumar kula da sadarwa ta Nigeria wato NCC ta koka kamfanin matambayi baya bata na google akan samar da service na wifi a kyauta a wasu sassan kasar nan. Hukumar dai ta zargi kamfanin na google da fara bayar da service din ba bias kaida ba.
Idan dai baa manta ba kamfanin na google na google ya fara aikin samar da service din na kyauta tun shekarar da ta gabata, wanda suka fara da jahar lagos , daga baya suka fadada shi zuwa Abuja. Kamfanin na google dai yayi alkawarin bunkasa service din zuwa wasu jahohi biyar a shekarar 2019. Ana sa ran dai mutane miliyan goma ne zasu amfana da tsarin. Sauran state din da ake sa ran samun service din sun hada da Kaduna, port harcout {rivers state} Ibadan {oyo state} enugu da Abuja.
Sai dai wani report da hukumar ta ncc ta shigar ta bayyana cewa kamfanin na google ya fara samar da service din ba bias qaida ba, hakan na kunshe a wata wasika da hukumar ncc din ta aikawa gwamnatin tarayya ta hannun hukumar presidential enabling business environment council {pebec}
Hukumar tan cc ta kuma zargi kamfanin na google da cewa basu mallaki takardar shaidar samar da internet a kasar ba wato internet service provider {isp} licence.

