-->

Wednesday, 2 May 2018

UC WEB SUN KARO WULAKANCI

Shahararren kamfanin nan na UCWEB wadanda suka kirkiri UC Browser sun karo wulakanci ta hanyar kirkirar wani sabon application na Android da iOS wanda amfani da shi wajen tura hotuna, waqoqi, da fina-finai cikin dan ƙaramin lokaci tamkar xender ko gionee xender.

Application din yana da bala'in saurin tura abubuwa kuma baya da nauyi ko kadan don gaba dayan application din MB daya ne kacal, kenan ba zai sambaɗe maka data wajen downloading ba. Haka kuma ba zai mamaye maka memory na ram din wayarka ba.   Yana daga cikin amfanin application din zaka iya amfani da shi a matsayin file manager, wato wurin da zaka rika shiga don nemo files din ka na kan waya da na kan memory card.

Harwayau zaka iya controlling data dinka ta hanyar kunnawa da kashewa daga cikin application din.   Idan ka shiga app din zaka ga music wanda anan ne zaka ga dukkan audio files dinka, sai video anan zaka ga duk videos dinka haka nan hotuna ma. Idan kuma folders kake son budewa sai kayi clicking akan files anan zai nuna maka dukkan folders dinka.   Bugu da kari kuma za ku iya amfani da shi wajen sharing na data ta hanyar amfani da Hotspot kamar dai yadda ake yi a xender.   Idan mutum daya yayi download na app din to zai iya amfani da Bluetooth wajen tura ma dukkannin abokansa... 

Ga mai bukatar application din sai ya hanzarta shiga Google playstore yayi searching na UCShare ko kuma ka shiga nan kayi downloading. 

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne. 

© Copyright SirrinWaya 2018,   
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner