-->

Wednesday, 27 December 2017

SOFTWARE 10 ZAFAFA

ANDROID APPLICATIONS GUDA GOMA WADANDA BABU KAMAR SU

Kusan dukkan android applications da muke amfani da su yau da kullum babu wanda yake shi kadai, ko amfanin me application yake yi maka to zaka samu akwai wani me irin wannan amfanin Kodai a Google play store ko kuma wasu apk websites din (torrent website). Wannan yasa android application developers suke competition da junansu wajen inganta Applications din su, shi yasa zaka ga kusan kullum suke updating applications din. Duk Kaga an yi updating application kuma to lallai Kodai ya kasance an kara masa wasu fa'idoji ko kuma an cire masa wasu matsaloli ko kuma duka.



A yau zamu dan tsakuro wasu applications da muke amfani da su yau da kullum mu yi bayanin fifikon su ga saura.

APPLICATION NA 1
CHROME BROWSER
Chrome browser: Kalmar browser an cirota ne daga kalmar browse wadda take nufin bincike, don haka ake kiran duk wata software wadda ake amfani da ita wajen bincike a duniyar yanar gizo da suna browser. Misalin browsers da muka fi amfani da su sun hada da chrome browser, Mozilla Firefox, opera mini, uc browser da sauran su, sai dai ni wadda nafi amincewa da ita itace chrome browser.
Chrome browser manhajar kamfanin Google ce, kuma kowa ya san Google su ne wadanda suka kirkiro da Android operating system ma gaba daya. Wannan yasa duk kamfanin da zai kirkiri wayar Android to tilas ya sayi Android operating system daga kanfanin Google. Wannan ne yasa kamfanin suka kware wajen sarrafa manhajojin Android, kasan an ce mai abu da abin sa.
Fifikon chrome akan sauran browsers shine duk fejin da kayi kokarin budewa da chrome ka ga ya gagara budewa kuma ka tabbatar ba daga network signals bane daga browser ne, to ina baka shawara kar ka bata lokacin ka jaraba wata browser din don babu browser din da zata bude maka shi, sai dai kawai ka yi amfani da computer kai tsaye.
Yana daga cikin matsalar chrome bata saving page for offline, sannan idan ka bude pages kana son kayi baya to sai ta sake loading da sauran su.

Zaka iya downloading anan https://play.google.com/store/apps/details?id=com.android.chrome

APPLICATION NA 2
XENDER
A bangaren sending abubuwa ma akwai su da dama amma ni wadda nayi recommending itace Xender. Babban abinda yafi burge ni da Xender shine tana da wani feature wanda bamu cika amfani da shi ba wato "phone replicate" shi wannan feature din zai baka dama kayi copying komai da ke kan wata waya zuwa wata wayar.
MISALI
Kana amfani da waya, bayan ka loda mata files naka sai ka canja wata, to anan zaka iya kwashe duk kayanka ka maida su akan sabuwar wayar tun daga music, videos, messages, contacts, notes Kai har settings dinka.

YADDA AKE PHONE REPLICATION DA XENDER
◀▶Da farko ka tabbata dukkan wayoyin biyu anyi installing xender a cikin su.
◀▶Daga nan sai kayi launching xender da duk wayoyin, ma'ana ka bude xender application.
◀▶Bayan ka bude xender sai kayi clicking akan dan circle (xender DP) din nan dake can saman screen daga gefen hannunka na hagu.
◀▶Zata nuna maka options kamar haka:
Ranking
More
Connect to PC
Phone replicate
Da sauran su

◀▶Sai kayi clicking phone replicate
◀▶Zata baka option biyu kamar haka "OLD" "NEW"
◀▶Wayar da kake son kwafar files din cikinta sai kayi clicking "OLD" nan take zata fara searching sabuwar.
◀▶Wayar kuma da kake son loda ma kayan sai kayi clicking "NEW"
◀▶Nan take sabuwar wayar zata tambaye ka kamar haka:
Old phone is an android
Old phone is an iPhone
◀▶Sai ka zaba idan tsohuwar wayar Android android ce ko iPhone.
◀▶Da zaran ka zabi operating system dinka nan take zata kai ka feji na gaba, inda zata tambaye ka shin waccan sabuwar wayar ma tana dauke da xender? Karka bata lokaci anan tunda kana da xender already har kayi launching ma, kawai kayi clicking akan next.
◀▶Kana yin clicking akan next zaka ga ta sanya maka wata alama kamar kayi creating (send) zaka tura wani abu.
◀▶Daga nan sai ka koma kan tsohuwar wayar ka wadda ke searching sabuwar wayar already. Anan take zasu yi connecting da junansu, sai tsohuwar ta fara antaya ma sabuwar dukkan kayan da suke a cikin ta.

Da zaran sun kammala zaka ga sabuwar wayar tana dauke da dukkan abinda waccan tsohuwar take dauke da shi, irin su settings, wallpapers, applications, music, videos da sauran su.

NOTE
Wannan bayanin baki daya an yi shi akan xender ne, don haka ban ce yana yi da gionee xender ko senderit ba. Ehe
Wannan shi ake kira phone replication.

Zaka iya downloading anan https://play.google.com/store/apps/details?id=cn.xender


APPLICATION NA 3
ENGLISH
English wani gagararren dictionary ne wanda har yanzu an kasa samun Android dictionary da zai kama kafar sa ballantana ya shiga gabansa. Developers na wannan application sun kai matuka wajen kawata shi da wasu specs wanda ba kowane developer bane yake iya wannan gagarumin aiki.

Kadan daga cikin abubuwan da English dictionary ya wuce sa'a dasu sune

1- Na daya kusan duk kalmar da zai baka ma'anar ta zai baka ma'anar ta tare kishiyar ta (opposite or antonyms)
2- zai baka kalmomin da suke kama da ita wato (synonyms),
3- zai baka asalin yadda aka samo asalin kalmar (origin)
4-Zai baka transcript na kalmar
5- Zai kuma sanya maka muryar baturiya ta karanta maka yadda ake pronunciation na kalmar, Kaga baka da bukatar koyon yadda ake pronouncing wata kalmar turanci.
6- Duk kalmar da ka duba zai ajiye maka ita a history
Zaka iya marking duk kalmomin da suka fi kayatar da kai a favourite
7- Duk kalmar da zai baka ma'anar ta idan sunan dabba ne zai baka zoological name nata, idan sunan tsirrai ne zai baka botanical name nasu.
8- Duk yawancin kalmomin da zai baka ma'anar su to sai ya fassara maka ita da French, Portuguese, Spanish.
9- Duk rana zai rika baka kalma daya wato word of the day, ta hanyar zabo irin kalmomin nan masu matukar wahala masu wahalar da turawa (verbose words) yana baka ma'anar su. A takaice idan ka maida hankali cikin kankanin lokaci sai kaji kana turanci tamkar Hilary Clinton.
10- Babban abinda yafi burge ni da Application din shine zai rika baka space karkashin kowace kalma inda zaka iya sanya bayaninka akan kalmar. Kamar ni yadda nake yi a karkashin kowace kalma sai ina fassara ta da Hausa, don haka dictionary na sai ya zama tamkar kamus, ga turanci, ga hausa, ga Spanish, Portuguese, ga French.

Zaka iya downloading anan https://play.google.com/store/apps/details?id=livio.pack.lang.en_US

APPLICATION NA 4
VLC PLAYER
VLC player wata player ce wadda ta sha bambam da sauran sa'anninta ta bangare da dama.

MISALI
1- Zaka iya sauraren video in background wato tamkar dai audio
2- VLC tana playing audio da video
3- Zaka iya amfani da VLC wajen kara ma waka ko video sauri ko nawa, wato zaka iya sanya video ko audio a slow motion.
4- Da VLC zaka iya hada Playlist na wakokin da kake bukata tayi maka playing kawai, idan sun kare ta kashe kanta ko kuma ta maimaita ya danganta da yadda kayi setting din ta.
Da dai sauran su.

Zaka iya downloading anan https://play.google.com/store/apps/details?id=org.videolan.vlc

APPLICATION NA 5
WPS OFFICE
WPS OFFICE wani application ne mai matukar amfani musamman ga dalibai, a takaice bazan iya kididdige iya abubuwan da zaka iya yi da wannan application din ba amma ga kadan.

1- Na farko dai reader ne ma'ana zaka iya amfani da shi wajen karanta kusan duk wani ebook format kamar su PDF, TXT, DOC, DOCX, da sauran su

2- Zaka iya amfani da WPS wurin kirkirar dukkan ebook format da muka zayyana a sama.

3-Zaka iya encrypting ebook din ka wato ka sanya ma ebook din password ya zama babu wanda ya isa ya karanta abinda ka rubuta sai idan ka gaya mashi password na ebook din.

4- Zaka iya typing na duk abinda kake so kamar CV, Application letter, project, assignment da sauran su, idan wayar ka tana supporting printer kawai sai dai kayi printing idan bata supporting sai ka kai computer ta yi maka printing kawai.

5- Zaka iya canza ma ebook format daga TXT zuwa PDF ko daga PDF zuwa DOCX ko daga DOCX zuwa DOC.

Zaka iya downloading anan https://play.google.com/store/apps/details?id=cn.wps.moffice_eng

Wannan kadan kenan daga abinda ya sawwaka, insha Allahu rubutu na gaba zamu karasa kawo maku cikon Applications biyar da suka rage.

Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.

©Copyright Sirrin Waya 2017
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
NEXT ARTICLE Next Post
PREVIOUS ARTICLE Previous Post
 
Get it on Google Play

Delivered by FeedBurner