A cigaba da kokarin da kamfanin Airtel ke yi don ganin sun rike customers din su tare da jawo wasu ma, yanzu sun kara yunkurowa da wani sabon salon sanyaya rayuwar abokan huddar su, saboda haka idan kai mutum ne mai sha'awar kallo da downloading din fina-finai ne irin su Indian films, American films, Ghanaian films, Kung-fu da television series to matso kusa ga wata sabuwar garabasa.
Wata sabuwar software kamfanin Airtel ya kirkira mai kamar YouTube ko kuma in ce tafi YouTube ma. Dalilin da yasa nace kamar YouTube take saboda irin tarin dubunnan videos na fina-finai da software din ta kunsa. Kuma wani abin farin ciki zaka iya amfani da software din wajen kallo da downloading kowane irin film ko da series ne kyauta ba tare da an caje ka sisin kwabo ba.
Don more garabasar maza ka shiga playstore kayi downloading NUVU Airtel Nigeria. Bayan kayi downloading sai ka shiga cikin software din, za su tambaye ka cewa sai kayi register, yes kayi clicking akan sign up zasu baka colum biyu na farko ka sanya email din ka sai na biyun ka sanya password din ka sai kayi sending. Zasu bukaci ka sanya lambar wayar ka ta Airtel sai ka sake sending.
Nan take zasu turo maka wasu lambobin a wayar ka ta message wato verification code sai kayi copying lambobin ka koma cikin NUVU ka sanya su. Anan zasu yi verifying din lambar ka. Daga sun yi verifying to ai hike nan a kafta.
KARIN BAYANI
Ka tabbatar cewa wani bai taba amfani da lambar ka yayi Nuvu registration da ita ba, saboda idan har an taba registration da ita to lallai ba zasu karbe ka ba saboda a ka'ida kowace lamba tana da nuvu free trial na tsawon kwanaki goma sha hudu ne. A cikin kwanaki sha hudun nan zaka iya kallon duk finafinan da kake bukatar kallo, zaka yi downloading duk abinda kake son downloading.
Sai dai kuma fa ku sani bayan ka cika wadannan Kwanaki sha hudun to ba zasu kara baka damar kallo ko downloading ba har sai kayi subscription na wata daya ko na sati daya. Nuvu subscription na wata daya Naira 1750 na sati daya kuma Naira 850.
WATA DABARA
Zaka iya cinye 14 days free trial din ka sannan kuma kayi login out ka sake sabuwar register ta hanyar amfani da wani layin wanda ba'a yi amfani da shi a baya ba. Sai dai kuma fa ban jaraba wannan trick din naga yana aiki ko baya yi ba.
Me tambaya yayi a karkashin comment box, mai sharing ko copying ma yayi amma lallai ya bayyana ya kwafo daga shafin mu ne.
© Copyright (sirrinwaya 2017)
WASU DAGA MUHIMMAN RUBUCE-RUBUCEN MU
GORON SABUWAR SHEKARA DAGA AIRTEL
